Sojojin Najeriya Sun Kashe Mayakan Boko-Haram da ISWAP

 

Rundunar sojin Najeriya ta ce sojojinta sun samu nasarar hallaka mayakan Boko Haram da ISWAP da dama a ranar Litinin, bayan daƙile wani yunkurin kwantan-ɓauna da suka so yi wa sojojin a kan hanyar Damboa zuwa Maiduguri na jihar Borno.

A wani sako da rundunar ta wallafa a shafinta na twita, ta ce ta kuma ƙwato makamai da dama da suka haɗa da jigidar harsasai da kuma babura.

Shugaban rundunar sojin Najeriya, Janar Faruk Yahaya, ya yabawa dakarun saboda jajircewarsu, inda ya bukace su da kada su yi kasa a gwiwa har sai an kawo karshen ‘yan tada-ƙayar-bayan da kuma wasu ayyukan bata gari a yankin arewa maso gabas.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here