Amsar da Kwankwaso ya Bayar Kan Ko Zai Amince da Sakamakon Zaben Shugaban Kasa Mai Zuwa Idan Bai Samu Nasara ba?

 

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP yace amincewa da shan kaye a zabe ba sabon abu bane a wurinsa.

Sanata Rabiu Kwankwaso ya yi jawabi a wurin taron da UNIABUJA ta shirya wa masu neman zama shugaban kasa a 2023.

Tsohon gwamnan Kanon ya ce zuwan NNPP cikin tseren ya samarwa yan kasa zaɓi baya ga APC da PDP.

Abuja – Rabiu Musa Kwankwaso, ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar NNPP ya ce ba shi da wata matsala game da amincewa da rashin nasara a zaɓe.

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa Kwankwaso ya bayyana haka ne a wurin taron mahawarar yan takarar shugaban kasa da aka shirya a jami’ar Abuja (UNIABUJA).

A fagen tambayoyi da amsoshi a wurin taron, wani ɗalibi ya tambayi Kwankwaso cewa ko zai amince da sakamakon zaben shugaban kasa mai zuwa idan bai samu nasara ba?

Da yake amsa wannan tambaya, tsohon gwamnan jihar Kano ya ce:

“A shekara 30 da ta wuce, na nemi takara sau 18, na yi nasara 15, na sha kaye sau uku, karo na farko da na sha ƙasa a zabe shi ne a 2003 lokacin ina kan kujerar gwamna.”

“Ina da yakinin ni ne gwamna ko shugaban kasa na farko, wanda ya sha kaye a zabe, ya ɗauki mataimakinsa, kwamishinoni da sauran manyan kusoshin gwamnati muka je taya wanda ya samu nasara murna har gida.”

“Saboda haka ban da wata damuwa wajen rungumar kaddarar rashin nasara a zaɓe. Na maimaita haka a Legas 2015 (zaben fidda gwanin APC) Buhari ya zo na ɗaya, na zama na buyu, Atiku na uku da Rochas na hudu.”

Tsohon gwamnan ya kara da cewa duk da ya san akwai matsaloli a zaben amma bai gardama ba ya amince da rashin nasara.

“Duk da haka fatana INEC da sauran masu ruwa da fsaki zasu yi abinda ya dace su shirya sahihi kuma karbabben zabe,” inji Kwankwaso.

Jaridar Pun ta tattaro Kwankwaso na cewa shigowar NNPP cikin jam’iyyu na sahun gaba ya baiwa yan Najeriya sabon zabi baya ga APC da PDP.

naija newspapers today

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here