Yadda Sojoji Suka Kashe ‘Yan Bindiga a Yankin Arewa
Sojojin sama sunyi nasarar lalata maboyar yan bindiga a maboyar su a dajikan Katsina da Zamfara.
An kai harin ne bayan samun rahotannin musamman da bayanan sirri kan maboyar.
Duka harin biyu an gudanar da su ranar 23 ga wata kuma an samu nasarar kawar da kusan yan bindiga 82.
Rundunar Sojojin Najeriya karkashin atisayen Hadarin Daji ta hallaka yan bindiga 82 a jihohin Katsina da Zamfara kamar yadda The Punch ta ruwaito.
Rundunar ta kuma kawar da yan ta’adda 67 a dajin Birnin Kogo da ke Katsina, sun kuma kawar da wasu 15 a dajin Ajjah da ke Zamfara.
Read Also:
Da ya ke bayyana haka a ranar Laraba a wata sanarwa mai taken, ‘Operation Hadarin Daji: Sojojin sama sun kakkabe yan bindiga a wani harin sama a dajin Birnin Kogo da kuma Ajjah a jihar Zamfara,’ mai magana da yawun hukumar, Manjo Janar John Eneche, ya ce harin da aka kai ranar Litinin, an yi shi ne gano maboyar su.
Anyi bayanin cewa jiragen sama da masu saukar ungulu mallakar rundunar sojojin sama sun yi barin wuta a inda ake zargi, kuma sunyi nasarar lalata kogunan da yan bindigar ke boya don kaucewa harin.
Sanarwar ta ce, “yan bindigar da ba su gaza 67, da suka mallaki manyan makamai, ciki har da bindigar baro jirgi, an murkushe su yayin da wasu da dama suka jikkata a wani harin sama da sojojin atisayen Hadarin Daji suka kai a dajin Birnin Kogo da ke jihar Katsina.
“A irin wannan hari, kusan yan bindiga 15 aka wargaza a makamancin harin da ya gudana a dajin Ajjah da ke jihar Zamfara.
“Duka harin guda biyu an gudanar da su ranar 23 ga watan Nuwambar 2020, bayan bibiyar rahotanni na musamman da saka idano wanda ya sa aka gano dajika biyu a matsayin maboyar, wanda ya janyo gano yan bindiga da daruruwan shanu da aka sace.”