Rundunar Sojojin Najeriya ta Magantu Kan Daukar Makamai Don Kare Kai Daga ‘Yan Bindiga
Rundunar sojojin Najeriya ta shawarci mazauna jahar Filato kan daukar makamai domin kare kansu sakamakon rigingimu da ake samu a yankin da ke tsakiyar Najeriya.
Shawarar da sojoji suka bayar na zuwa ne bayan ‘ƴan majalisar jahar sun bukaci al’umma su dauki makamai domin kare kansu, yayin da matsalar tsaro ke sake taɓarɓarewa a yankin.
Read Also:
Sama da mutum 60 ne suku mutu a hare-hare daban-daban da ‘ƴan bindiga suka kai a jahar a wannan watan na Agusta.
Ministan tsaro da wasu gwamnonin jahohi sun yi kira ga ƴan Najeriyar su kare kansu daga hare-haren ‘yan bindiga da masu sata domin neman kudin fansa.
Sai dai masu sharhi na cewa bai wa farar-hula damar daukar makami domin kare kansu tamkar nuna gazawa ce daga ɓangaren gwamnati da kuma dauke nauyin da ke kansu na kare al’umma.
Sannan akwai fargabar hakan sai sake taɓarɓare lamuran tsaro yayin da Najeriya ke laluben hanyoyin yi wa matsalolinta tufka.