Rundunar Sojoji ta yi Nasarar Kashe Wasu ‘Yan Bindiga

 

Rundunar soji ta ‘Operation Whirl Stroke (OPWS) ta hallaka mutane uku a wani barin wuta da suka yi a daren Lahadi.

An ruwaito cewa yan bindigar sun mamaye Adaka kuma suna yi wa mutanen yankin fashi.

Mazauna yankin sun bayyana cewa ba don sojoji sun kawo musu dauki ba, da abin ya munana.

Rundunar soji ta musamman ta ‘Operation Whirl Stroke’ (OPWS) ta hallaka mutane uku da ake zargin ‘yan bindiga ne a wani barin wuta da daren Lahadi da ya faru a yankin Adaka da ke Makurdi a jihar Benue.

Wasu daga cikin mutanen yankin, sun bayyanawa jaridar Daily Trust cewa ‘yan bindigar sun mamaye Adaka, wata unguwa a cikin garin Makurdi kuma suna yi wa mazauna yankin fashi kafin sojoji su ceto su.

An ruwaito cewa sojojin sun samu kira daga mazauna yankin lokacin da suke sintiri a yankin don kawar da yan bindigar, an yi barin wutar da yayi sanadiyar mutuwar mutane uku da ake zargin.

Mazauna yankin sun fadawa manema labarai a Makurdi cewa lamarin ya faru da misalin karfe 8:00 na dare, kuma ba don sojoji sun yi gaggawar kawo musu dauki ba da abin ya kazanta tunda har ana zargin ‘yan bindigar sun harbi wasu ma’aurata.

Da aka tuntubi babban kwamandan OPWS, Manjo Janar Adeyemi Yekini, ya tabbatar wa manema labarai cewa tawagar sintirinsa sun yi bata-kashi tsakanin su da ‘yan bindiga a Adaka.

“Jami’an mu a shirye suke kuma za su yi duk mai yiwuwa tare da sauran jami’an tsaro don kare al’umma,” a cewarsa.

Yekini ya kuma shaidawa manema labarai da su tuntubi mai magana da yawun hedikwatar tsaro don jin karin bayani a kan batun.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here