Rudunar Sojoji ta yi wa ‘Yan Bindiga Bazata

Rundunar Sojojin Operation Thunder Strike, OPTS, a daren Juma’a ta kawar da yunkurin da yan bindiga sukayi na garkuwa da mutane a hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Gwamnatin jihar Kaduna ta samu bayani daga jami’ai cewa yan bindiga sunyi kokarin kai hari a yankin Kasarami dake karamar hukumar Chikun misalin karfe 7:38 na dare.

Kwamishanan harkokin tsaron jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya saki jawabi cewa Sojoji na kan sintiri sukayi arangama da yan bindigan.

Jawabin yace yan bindigan sun gudu yayinda Sojoji suka kure musu gudu. “Da dama cikin yan bindigan sun gudu da raunukan daga harsasai.Sojoji na binsu kuma za’a sanar da al’umma kan yadda ake ciki,” yace

“Sauran Sojojin na kan hanyan domin bude hanyar da ta toshe sakamakon musayar bindigan.”

“Gwamnatin jihar Kaduna na mai bada hakuri ga matafiya da suka fuskanci bacin lokaci sakamakon harin Sojojin. An yi hakan ne domin kare rayuka da dukiya,” Aruwa ya kara.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here