Sojojin Ruwan Senegal Sun Ceto ‘Yan Cirani 80
Sojojin ruwan Senegal sun kubutar da ‘yan cirani sama da 80 a gabar tekun yammacin Afrika, kamar yadda kamfanin dilancin labarai na AFP ya ruwaito.
Read Also:
Rahoton ya ce jirgin ruwan ‘yan cirani ya kife ne lokacin da suke kokarin zuwa tsibirin Canary da ke cikin ƙasar Spaniya.
Jirgin ruwan ya tashi ne daga kasar Gambiya ranar Litinin kuma wani jirgin saman sojin Spaniya ne ya gan shi a cewar AFP. Daga nan ne kuma ya fara nutsewa.
Wasu jiragen ruwa biyu ne suka kwashe mutanen 82 a tekun Atlantika mai nisan kilomita 86 daga gaɓar tekun Senegal.