Kamfanonin Sufurin Jirgin Sama Sun Soke Sauka da Tashin Jiragen Saboda Tsadar Man Fetur a Najeriya
Da alama babu sauki nan kusa kan batun tsadar man fetur a Najeriya, matsalar da ta tilasta wa kamfanonin sufurin jirgin sama kara farashin tikitinsu a kwanakin baya.
Kamfanonin sun ce a jiya sun yi mamaki bayan da aka sanar da su cewa an kara farashin man jirgin saman, inda ake sayar da shi kan naira 607 kan kowace lita a Kano a jiya.
Wannan ya kasance karin fiye da naira 100 cikin kwana guda.
Read Also:
Jaridar Daily Trust ta ce wasu masu kamfanoni sufurin jiragen saman sun sami sanarwar ce daga masu dillancin man a jiya, wadda ke sanar da su cewa farashin man na JetA1 ya karu zuwa naira 597 a Legas, kuma ya koma naira 599 a Abuja da Port Harcourt, sannan ya koma naira 607 a Kano.
A ranar Litinin an rika sayar da man kan naira 470 ne a Legas, inda a Kano kuwa naira 495 aka sayar da shi.
Wannan matakin ya janyo soke sauka da tashin jiragen sama a manya da kananan filayen jirgin sama na Najeriya.
Yawancin kamfanonin sufurin jirgin saman sun fitar da sanarwar da ke bayana halin da suka shiga kuma sun ba abokan huldarsu hakuri.
Kakakin kamfanin Azman Airline ya koka kan halin da suka sami kansu a ciki kuma ya ce babu yadda za su iya mayar da uwar kudin da suke zubawa balle ma su sami riba.