Bincike ya Gano Cewa Har Yanzu ba a Soma Aikin Tashar Wutar Lantarkin Mambila ba
Shekaru kusan 40 da bada kwangilar Mambila, har yanzu babu abin da aka tabuka.
Idan aikin ya kammala, Najeriya za ta samu karin karfin wuta na megawatt 3, 000.
A halin yanzu mutane miliyan 200 a kasar suna raba megawatt 5,000 zuwa 5400 ne.
Taraba – BBC Hausa ta gudanar da wani bincike na musamman a kan tashar wutar lantarkin Mambila inda ta gano cewa har yau ba a soma wannan aikin ba.
Shekara 39 kenan da gwamnatin shugaba Shehu Shagari ta bada kwangilar samar da wutar lantarki ta tashar Mambila, kawo yanzu babu labarin wannan aiki.
A shekarar 1982 aka tsara cewa tashar za ta samar da megawatt 2600 na karfin wuta idan an gama aikin.
Amma da ‘dan jaridar BBC ya ziyarci tashar, sai ya gano cewa ba a fara yin aikin ba. ‘Dan jaridar ya je har gangaren ruwa na Tambi wanda yana cikin tsarin tashar.
Read Also:
Duk da cewa mota ba ta iya zuwa wannan wuri, ‘dan jaridar ya hau babur, inda ya shafe sa’o’i biyar yana tafiya, daga baya sai ya karasa tashar lantarkin a kafa.
Shekara da shekaru babu labari
Shugabanni goma aka yi a Najeriya amma ba su iya cika alkawarin da aka yi ba. Shugabannin su ne; Shehu Shagari, Muhammadu Buhari da Ibrahim Babangida.
Sai Ernest Shonekan, Sani Abacha da Abdussalami Abubakar. Daga nan sai Olusegun Obasanjo, Ummaru ‘Yar’adua, Goodluck Jonathan sai Buhari (ya dawo).
Har yanzu aiki bai kankama ba?
Rahoton yace mafi yawan hotunan da ake gani a shafukan yanar gizo a kan wannan aiki, na bogi ne.
Mutane suna dauko hotunan takwarar tashar Mambila, madatsar ruwar Kashimbila (duk a jahar Taraba), suna yada wa da sunan tashar wutar lantarkin Mambila.
A wata hira da aka taba yi da Injiniya Saleh Mamman a lokacin yana Ministan wutar lantarkin Najeriya, yace batun wannan aikin tamkar tatsuniya ce kurum.