Suarez ya yi Ritaya Daga Buga wa ƙasarsa Kwallo

 

Ɗan wasan gaban Urguay Luis Suarez ya yi ritaya daga bugawa ƙasarsa kwallo.

Dan wasan mai shekara 37 ya ɓarke da kuka lokacin da yake sanar da cewa wasan da zai bugawa ƙasarsa a ranar Asabar na neman gurbi a kofin duniya da Paraguay zai zama na ƙarshe a tarihi.

Tsohon ɗan wasan Liverpool da Barcelona wanda kuma shi ne ya fi kowa cin kwallo a tarihin Urguay inda ya ci kwallo 69 a wasa 142 da ya buga, ya kuma fara bugawa Uruguay wasa ne a 2007 a wasan Urguay da Colombia.

“Na yi ta tunanin kan wannan matakin ina ta hasashen yadda za a yi. A ganina wannan ne lokacin da ya kamata,” in ji Suarez.

“Ina son hutawa idan na gama wasana na ƙarshe. Ina son jin dadin wasan irin wanda na ji ranar da na fara buga wasa a 2007,” in ji shi.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here