Sunayen Kwamishinoni 53 da Suka yi Murabus Daga Mukamansu a Jahohi 7
Kamar yadda tanadin sashi na 84, sakin layi na 12 ya tanadar na gyararrun dokokin zabe, a kalla kwamishinoni 53 da wasu hadiman gwamnonin jiha ne suka yi murabus daga mukamansu domin neman kujerun siyasa kafin zuwan zaben 2023.
Wannan na zuwa ne bayan ministoci a matakin tarayya da suka hada da Rotimi Amaechi, Sanata Chris Ngige, Abubakar Malami da wasu shugabannin cibiyoyin tarayya da ke hango kujerun siyasa suka yi mirsisi suka ki murabus.
Yayin da Amaechi tuntuni ya bayyana burinsa na gaje Buhari, Malami kamar yadda majiyoyi makusantansa suka sanar, zai nemi kujerar gwamnan jiharsa. Daily Trust ta ruwaito cewa, shugabannin cibiyoyin tarayya da ke hararo kujerun gwamna, Sanata da ‘yan majalisun tarayya suna da yawa.
Darakta janar na NIMASA, Bashir Yusuf Jamoh, a kwanakin karshen mako ya fara tuntubar jama’a domin fitowa takarar kujerar gwamnan Kaduna.
Sunaye da masu mukaman da suka yi murabus yayin da suke son fitowa takara:
Kwara
A kalla kwamishinoni da hadiman Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq na jihar Kwara ne suka yi murabus domin neman kujerun siyasa a zaben 2023.
Sun hada da:
1. Kwamishinan ilimi da cigaban dan Adam, Hajia Sa’adatu Modibbo-Kawu
2. Kwamishinan sha’anin hada-hada, Hajia Fatimah Arinola Lawal
3. Mai bai wa gwamna shawara na musamman kan ayyuka na musamman, Alhaji Yinka Aluko
. Mataimaki na musamman ga gwamnatin kan habaka ma’adanai, Dr Mohammed Abubakar
5. Kwamishinan shari’a, Salman Jawondo
6. Kwamishinan hakar ma’adanai, Harriet Afolabi-Osatimehin
7. Mai bada shawara na musamman kan tallafin al’umma, Kayode Oyin-Zubair
8. Babban manajan KWASSIP, Mohammed Brimah
9. Kwamishinan lafiya, Dr Raji Razak
10. Alhaji Abdulateef Alakawa, mai bada shawara ga gwamna kan lamurran siyasa
Read Also:
11. Kwamishinan ayyukan noma, Sabba Yisa Gideon
Kano
A kalla kwamishinoni 10 ne suka yi murabus, sun hada da:
1. Kwamishinan ruwa, Sadiq Wali
2. Mataimakin gwamna, Nasir Gawuna
3. Kwamishinan kananan hukumomi da lamurran sarautar, Murtala Suke Gari
4. Kwamishinan kasafi da tsaro, Alhaji Nura Muhammed Dankade
5. Kwamishinan yawon bude ido, Sanusi Said Kiru
6. Kwamishinan ayyuka na musamman, Ibrahim Ahmad Karate
7. Kwamishinan habaka karkara, Iliyasu Kwankwaso
8. Kwamishinan sufuri, Mahmoud Muhammad Santsi
9. Kwamishinan lafiya, Aminu Tsanyawa
10. Shugaban ma’aikatan fadar gwamna, Ali Haruna Makoda
Delta
A jihar nan, shugaban ma’aikatan fadar gwamnan da wasu kwamishinoni tara ne suka yi murabus.
Akwa Ibom
1. Kwamishinan habaka tattalin arziki, Akan Okon
2. Kwamishinan ayyukan gona, Glory Edet
3. Kwamishinan cinikayya da hannayen jarj, Baristw Prince Akpabio
4. Kwamishinan ayyuka na mhsamman, Okpulupm Etteh
5. Kwamishinan ayyuka, Farfesa Enoh Ibanga
6. Kwamishinan filaye da ruwa, Umo Eno
Benue
1. Shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin, Fasto Terwase Orbunde
2. Sakataren yada labarai, Terver Akase
3. Kwamishinan yada labarai, al’ada da yawon bude ido, Ngunan Addingi
4. Kwamishinan muhalli da ruwa, Engr Dindo Ahire
5. Kwamishinan ilimi, Farfesa Dennis Ityavyar
6. Kwamishinan matasa da al’adu, Kwamared Ojemba Ojotu.
Rivers
1. Sakataren gwamnatin jihar, Dr Tammy Danagogo
2. Kwamishinan kudi, Isaac Kamalu
3. Kwamishinan wasanni, Boma Iyayi
4. Mai bai wa gwamnatin shawara na musamman kan ayyuka na musamman, George Kelly
5. Babban akawun jihar, Asimilaye Fubara.
Kaduna
Kwamishinan tsari da kasafi ne kadai, Mohammed Sani Abdullahi, wanda aka fi sani da Dattijo, shi ne mutum daya da yayi murabus.