2023: Za ka Sha Kaye, Amma za ka Zama Mai Karban Faduwa da Zuciya Daya – Ganduje ga Wike

 

Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas na ci gaba da tuntuban yan arewa a kokarinsa na son ganin ya gaje Shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben 2023.

Wike ya ziyarci takwaransa na jihar Kano, Abdullahi Ganduje a ranar Litinin, 18 ga watan Afrilu.

Sai dai Ganduje ya kalli Wike cikin ido sannan ya sanar masa cewa ba zai kai labari ba a zaben.

Amma kuma ya ce yana birge shi saboda irin karfin gwiwar da yake da shi domin hakan ne zai basa damar sake gwada sa’arsa a gaba.

Kano– Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya kalli takwaransa na jihar Ribas, Nyesom Wike a cikin ido sannan ya sanar masa da cewa ba zai yi nasara ba a kokarinsa na son gaje shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben 2023.

Ganduje ya yi sakin zancen ne a lokacin da Wike ya ziyarci jiharsa a yayin da yake ci gaba da tuntubar al’umman yankin arewacin Najeriya domin samun goyon bayansu.

Sai dai kuma cike da barkwanci, Gwamna Ganduje ya ce Wike na birge shi saboda kasancewarsa daga cikin mutane masu karfin gwiwa, wanda koda sun fadi a yau za su sake tashi domin sake gwada sa’arsu a gaba.

A cikin wani bidiyo wanda tuni ya karade yanar gizo, an jiyo Ganduje yana cewa:

“Wato, ka zo ganin yan uwanka maza da mata. Ya yi kyau. Kana neman takarar shugaban kasar Najeriya. Mun ga kokarinka.

“Sannan a karshe, za ka sha kaye, amma za ka zama mai karban faduwa da zuciya daya. Ina son masu karban faduwa da zuciya daya saboda suna da karfin gwiwa. Kuma tunda kana yin abun cikin lumana, za ka yi nisan kwana domin sake gwadawa. Ina taya ka murna, Mai hikima Wike.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here