Allah ya yi wa Mahaifiyar Abubakar Idris Dadiyata Rasuwa

Allah ya yiwa Malama Fatima, mahaifiyar Abubakar Idris Dadiyata wanda wasu da ba a san ko su waye ba suka sace shi, rasuwa.

Marigayiyar ta amsa kiran mahaliccinta ne a safiyar yau Talata, 19 ga watan Afrilu, bayan ta yi fama da rashin lafiya.

Wasu makusanta da abokan Dadiyata sun tabbatar da labarin mutuwar tata a shafukansu na sadarwa

Kaduna- Labari da ke zuwa mana shine cewa Allah ya yiwa Malama Fatima, mahaifiyar Abubakar Idris, wanda aka fi sani da Dadiyata, rasuwa.

Jaridar Aminiya ta rahoto cewa Malama Fatima ta rasu ne a safiyar yau Talata, 19 ga watan Afrilu, bayan ta yi fama da jinya a asibitin sojoji na 44 da ke jihar Kaduna.

Rahoton ya kuma kawo cewa wani makusancin iyalan, Lawal Muhammad, ya tabbatar da cewar an garzaya da marigayiyar zuwa asibiti ne da asubahin yau sakamakon tsanani da jikin nata ya yi.

Malam Lawal wanda ya kasance amini ga yayan Dadiyata, Usman Idris, ya ce a yanzu haka, abokin nasa na a hanyarsa ta komawa Kaduna, bayan ya samu labarin rasuwar mahaifiyar tasu.

Wani abokin Dadiyata mai suna Ibrahim Adam ya sanar da labarin mutuwar a shafinsa na Twitter yana mai cewa:

“Mutuwa ta dauke mahaifiyar abokinmu Dadiyata da ya bata. Allah ya ji kanta

Nasiru Fulatan

@nkfulatan ya rubuta a shafinsa:

“Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun! Dan uwanmu kuma abokinmu da aka sace Abubakar Idris Dadiyata ya rasa mahaifiyarsa a yau.Ina mika ta’aziyyata ga iyalansu baki daya.

Allah ya basu juriyar daukar wannan rashi Allah ya mata rahama!”

Legit Hausa ta nemi jin ta bakin wani abokin Dadiyata mai suna Mallam Malumfashi inda ya nuna alhini tare da addu’an Allah ya bayyana abokin nasa.

Ya ce:

“InnalilLahi wa inna ilaihi rajiun!!! Allah ya isa!! Allah ya yafe mata. Allah bayyana shi.”

A ranar 2 ga watan Agusta, 2019, ne wasu mutane da har yau ba a san su wanene ba, suka dauke wannan matashi da ake kira Dadiyata, har yau babu labarinsa.

Dadiyata wanda malamin makaranta ne ya bar iyalinsa da ‘ya ‘ya biyu

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here