Duk Masu Sukar Shugaba Buhari Kan Halin da Ake Ciki to da Alama Suna Taimaka wa ‘Yan Bindiga ta Wata Hanya – Gwamna Uzodinma

Gwamna Uzodinma na jihar Imo ya ɗora ayar tambaya kan masu ganin laifin shugaba Buhari game da taɓarɓarewar tsaro.

Gwamnan ya ce duk masu sukar shugaban kasa kan halin da ake ciki to da alama suna taimaka wa yan bindiga ta wata hanya.

Mista Hope Uzodinma ya kuma fallasa yan siyasan da yake zargin suna rura wutar matsalar tsaron jiharsa ta Imo.

Imo – Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo ya ƙi yarda da masu zargin cewa shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya kamata a ɗora wa laifin taɓarɓarewar tsaro a Imo.

Gwamnan ya bayyana cewa duk masu kalar wannan tunanin da alamu suna da hannu ta karkashin kasa a ayyukan yan bindiga, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Uzodinma ya kuma ankarar da cewa a halin yanzun mambobin APC a Imo sun koma abun harin wasu yan siyasa da abokan haɗin guiwarsu, waɗan da ke taimakawa yan bindiga da masu kisan kai.

Gwamnan ya yi wannan furucin ne a wurin ɗaura auren ɗan fitaccen ɗan kasuwan nan kuma ɗan siyasa, Emmanuel Iwuanyanwu, wanda ya gudana a wata Coci dake Owerri ranar Litinin.

Ya ce sheɗanun yan siyasa sun kuduri aniyar lalata jihar Imo ta hanyar kashe mutane haka nan, da kuma ƙona kayan gwamnati da masu zaman kansu kuma duk da sunan siyasa.

Ya roki Cocin da sauran taron mutane su cigaba da sa irin waɗan nan mutane a addu’o’insu ko Allah zai sa su tuba.

Tsaron Imo na da alaƙa da siyasa – Uzodinma

Da yake a jawabi a gaban taron Jama’a a wata Coci a ƙaramar hukumar Oru ta gabas, tun ranar Lahadi, Uzodinma ya ce ƙashe-kashen dake faruwa na da alaƙa da siyasa.

Ya ce:

“Ina fatan shiriyar Allah ta shiga zuciyar mutanen dake taimaka wa wajen ƙashe-kashen mutane, ƙona gidaje da lalata kadarorin gwamnati duk da sunan siyasa.”

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here