Taliban na Kulle Matan da Suka Tsira Daga Cin Zarafi a Gidan Yari

 

Wani rahoton Majalisar Ɗinkin Duniya ya ce gwamnatin Taliban a Afghanistan na kulle matan da suka tsira daga cin zarafi a gidan yari tare da iƙirarin cewa tana yin haka ne domin kare su.

Majalisar Ɗinkin Duniyar ta ce matakin na shafar lafiyar ƙwaƙwalwar matan.

Rahoton ya ce babu sauran matsugunai na mata da gwamnati ke ɗaukar nauyinsu yayin da gwamnatin Taliban ke ganin babu buƙatar irin waɗan nan cibiyoyin.

Wani shirin tallafa wa al’umma a Afghanistan na Majalisar Ɗinkin Duniy UNAMA, ya ce cin zarafin da ake yi wa mata da ƴan mata a Afghanistan yana da yawa tun kafin Taliban ta ƙwace gwamnati.

Sai dai tun lokacin, irin waɗan nan matsalolin sun sake zama ruwan dare ganin tasirin tattalin arziki da kuma matsalolin jin ƙai da suka shafi ƙasar, kamar yadda UNAMA ta ce.

An ci gaba da tsare mata a gidajensu abin da ke daɗa jefa su cikin haɗarin fuskantar cin zarafi daga abokan zamansu.

Kafin Taliban ta ƙwace mulki a 2021, akwai cibiyoyin kare mata 23 da ke ƙarƙashin gwamnati a Afghanistan amma a yanzu babu waɗan nan cibiyoyin.

Jami’an Taliban sun faɗa wa UNAMA cewa babu buƙatar cibiyoyin saboda matan suna tare da mazajensu ko ƴan uwansu maza.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com