Kungiyar Taliban ta Nada Sabon Firayim Minista na Kasar Afghanistan
Kungiyar Taliban ta nada Mullah Mohammad Hassan Akhund a matsayin sabon Faraim Minista na kasar Afghanistan.
Zabihullah Mujahid, mai magana da yawun kungiyar ta Taliban ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar.
Taliban ta kuma nada wasu sabbin ministocin rikon kwarya cikinsu har da Mullah Yaqoob dan tsohon shugaban Taliban Mullah Omar.
Afghanistan – Kungiyar Taliban ta sanar da Mullah Mohammed Hassan Akhund a matsayin sabon shugaban gwamnatinta a Afghanistan a yau Talata, The Punch ta rawaito.
Babban mai magana da yawun kungiyar Zabihullah Mujahid ya shaidawa manema labarai ya sanar da cewa wanda aka kafa Taliban da shi Abdul Ghani Baradar shine zai zama mataimakin shugaban kungiyar.
Su wanene sabbin ministocin da Taliban da nada?
A cewar kakakin na Taliban sabon ministan harkokin cikin gida shine Sarajuddin Haqqani kamar yadda LIB ta rawaito.
Read Also:
Sauran nade-naden sun hada da Mullah Yaqoob a matsayin ministan tsaro na riko, Amir Khan Muttaqi a matsayin ministan riko na harkokin kasashen waje sai Mullah Abdul Ghani Baradar and Mullah Abdul Salam Hanafi a matsayin mataimakansa biyu.
Yaqoob shine dan wanda ya kafa Taliban marigayi Mullah Omar.
A baya, Baradar ne shugaban ofishin siyasa na Taliban wanda ya ratabba hannu kan yarjejeniya da Amurka na ficewa daga kasar a bara.
Sabon ministan harkokin cikin gidan yana jerin mutanen da FBI ke nema ruwa a jallo duba da shine shugaban kungiyar masu tada kayar baya na Haqqani wadanda ke da alaka da Taliban kuma sun kai hare-hare da dama yayin yakin da aka shafe kimani 20 ana gwabzawa.
Taliban ta kwace mafi yawancin sassan kasar kimanin makonni uku da suka gabata, ta hambarar da tsohon zabebben shugaba Ashraf Ghani.
Kakakin na kungiyar Taliban, Zabihullah Mujahid ya kara cewa kungiyar ta amsa bukatan mutane yana mai cewa:
“Mun san mutanen kasar mu sun dade suna jiran ganin sabuwar gwamnati.”