Shugaban ƙasar Tanzania ya yi iƙirarin kawar da cutar coronavirus

 

Tsarin da Shugaban Tanzania, John Magafuli ya ɗauka na daƙile cutar korona ya sa ƙasar ta zama abin kallo a duniya. A halin yanzu, shugaban na neman tsayawa takara karo na biyu.

A lokacin da annobar korona ta ɓulla a Tanzania, Shugaba Magafuli bai yadda da mutane su zauna a gida ba. Yana so su koma masallatai da coci-coci domin gudanar da addu’o’i.

“Cutar korona wadda sheɗaniya ce ba za ta rayu a jikin mabiyan Yesu ba, za ta ƙone nan take”, in ji Magafuli, wanda Kirista ne kuma ya ayyana hakan a ranar 22 ga watan Maris na 2020 a Dodoma babban birnin ƙasar.

Nan gaba kaɗan zai yi magana kan bayar da tazara da kuma saka takunkumi, inda kuma yake saka ayar tambaya kan batun gwajin cutar bayan an yi gwaji kan dabbobi daban-daban da kayan lambu – shugaban ya bayyana cewa an samu cutar korona a jikin gwanda da kuma akuya.

Shugaban ya ce ba zai tsayar da harkokin kasuwancin ƙasar ba, duk da cewa wasu na sukar hanyar da ya bi ta shawo kan annobar.

Shugaban kuma ya bankaɗo ma’aikatan bogi da dama inda ya cire su daga tsarin albashi na ƙasar, tare da korar ma’aikatan da yake gani a matsayin waɗanda suke cin hanci ko kuma ba su yin aiki sosai.

Ya kuma rage yadda ake kashe kuɗin gwamnatin ƙasar inda ya soke taron bikin zagayowar ranar ‘yancin ƙasar karo na farko a shekara 54. A maimakon hakan, sai ya bayar da umarnin tsaftace ƙasar, inda ya yi amfani da hannunsa shi ma wurin tsince datti da kuma share titunan ƙasar.

Sai dai duk da hakan, ana ganin cewa akwai wani ɓangare mai duhu daga cikin mulkinsa – inda ake ganin wasu daga cikin tsare-tsarensa za su kawo matsala ga dimokraɗiyyar ƙasar.

Waƙar da ta zama gaskiya

A Janairun 2016, kusan watanni biyu da rantar da shi, gwamnatinsa ta bayyana cewa kafar yaɗa labarai ta ƙasar ba za ta ci gaba da watsa zaman majalisar ƙasar kai tsaye ba a yunƙurin rage kashe kuɗin gwamnati.

‘Yan adawa sun ɗauki wannan mataki a matsayin tauye haƙƙi kuma ta irin haka ne kawai za su san abin da gwamnati take ciki. ‘Yan adawan sun shirya yin zanga-zanga sai dai gwamnatin ƙasar ta fito ta haramta duk wata zanga-zanga a ƙasar.

Wani misali na irin hakan shi ne martanin da Magafuli ya mayar a 2017 kan waƙar wani shahararren mawaƙi na ƙasar Tanzania Nay wa Mitego. Jim kaɗan bayan fitar da waƙar, sai ‘yan sanda suka kama Mista Mitego.

An zarge shi da zagin shugaban ƙasar da faɗin munanan kalamai a kansa. Abubuwan da ya fadi a waƙar game da shugaban ƙasar sun fara faruwa – tuni dai aka rufe shi a babban ofishin ‘yan sanda na Dar es Salaam.

Duk da cewa shugaban ya bayar da umarnin sakin mawaƙin kwana ɗaya bayan faruwar lamarin, daga baya ya bayar da umarnin a sake rera waƙar domin saka wasu sabbin baituka da za su nuna matsalolin al’umma kamar cuta a wurin bayar da haraji da sauransu.

Gwamnatin Magafuli ta ci gaba da fitar da sabbin tsare-tsare da kuma kawo sabbin dokoki na ƙara haraji ga kamfanonin ƙasar waje da kuma na haƙar ma’adinai.

Gyara ɓangaren sufuri na Tanzania

Masu sharhi sun bayyana cewa Shugaba Magafuli ya kawo ci gaba a ƙasar ta hanyar zuba jari kan abubuwan more rayuwa kamar gina layin dogo na zamani wanda zai haɗa ƙasar da makwaftanta na yankin, da ƙara faɗaɗa manyan titunan ƙasar.

Shugaban ya ƙara haɓaka hanyar samar da wutar lantarki kuma hakan ya sa wutar ta ƙara wadata a ƙasar.

Shugaban ya kuma farfaɗo da kamfanin jirgin sama na ƙasar, Air Tanzania wanda a baya cin bashi da kuma riƙon sakainar kashi ya durƙusar da shi, inda ko a lokacin da shugaban ya hau mulki, jirgi ɗaya tak kawai ke aiki.

Da zuwan shugaban, sai ya naɗa sabon shugaban kamfanin da sabbin jami’ai inda aka ƙara sawo sabbin jirage guda shida domin su ci gaba da aiki.

Shugaban ƙasar ya kuma kawo tsarin ilimi kyauta ga duka makarantun gwamnati na Tanzania har zuwa aji huɗu na sakandare.

‘Na san mene ne talauci’

Magafuli ya dage wurin yaƙi da cutar korona a hanyarsa da ya fi yarda da ita, a maimakon biye wa abin da wasu ƙasashen yankin da kuma na duniya suke yi. Tsarin gudanar da gwamnatinsa ya yi kama da na tsohon shugaban ƙasar, Mwalimu Julius Nyerere, wanda shi ma shugaba ne mai zaman kansa.

“Shugaban ƙasarmu na farko mutum ne wanda ba a faɗa masa abin da zai yi. Waɗanda suke kawo irin waɗannan dokokin na saka dokar kulle shugaban ƙasarmu na farko ba ya bin umarnin su,” in ji Magafuli inda yake nuni da halin Shugaba Nyerere na watsi da shawara daga ƙasashen yamma.

Magafuli ya girma ƙarƙashin mulkin Nyerere a wani ƙauye da ke arewa maso yammacin ƙasar kusa da tafkin Victoria, inda ya ce kyakyawar tarbiyar da ya samu ne ya sa masa ra’ayin yi wa ƙasarsa aiki.

“Gidanmu gidan ciyawa ne, kuma kamar sauran yara, ana sa ni kiwon shanu, da kuma sayar da madara da kifi domin taimaka wa gidanmu,” kamar yadda ya bayyana a lokacin yaƙin neman zaɓe a 2015.

Bayan ya kammala makaranta, ya yi aiki na shekara guda a matsayin malamin koyar da lissafi da kuma ilimin sinadarai kafin ya koma makaranta ya ci gaba da karatu. Ya yi aiki na shekaru ƙalilan a matsayin jami’in kula da sinadarai a wani kamfani kafin ya yi murabus daga muƙaminsa ya yi takarar ɗan majalisa a 1995 a mazaɓarsa ta Chato.

Bayan ya lashe zaɓe, cikin gaggawa ya yi ta samun ƙarin girma har ya kai matsayin mataimakin ministan ayyuka.

Tafiya ta yi tafiya har zuwa 2015 a lokacin da Magafuli ke son tsayawa takarar shugaban ƙasa, an bayyana cewa an cimma matsaya inda aka tsayar da shi a matsayin ɗan takarar jami’iyyar CCM wadda ta shafe shekara 54 tana jagorantar ƙasar.

Masu sharhi sun bayyana cewa a matsayin Magafuli wanda asalinsa ba ɗan siyasa ba ne ya sa ya zama mutum mai amfani ga ƙasar, sunansa bai ɓaci da batun cin hanci da rashawa ba kamar sauran takwarorinsa.

Zaɓen ya yi zafi a ƙasar amma Magafuli ya yi ƙoƙari inda ya samu kashi 58 na ƙuri’u cikin 100

Barazanar fitowa a yi magana

A daidai lokacin da Tanzania ke tunkarar lokacin zaɓen sabon shugaba, an daina kiran da ake yi ga sabbin shugabannin yankuna su yi koyi da hali irin na Magafuli.

Shugaban ya fuskanci caccaka daga ƙungiyoyi masu zaman kansu da kuma ƙasashen yamma waɗanda ke cewa yana takura wa ‘yan adawa da kuma take haƙƙin ‘yan jarida da kuma cin tarar kamfanonin ƙasashen ƙetare.

Amma a matsayinsa na shugaban ƙasa mai kiran kansa mai kishin Afrika kuma riƙaken Kirista na ɗarikar Katolika, shugaban yana jan faɗa da kasashen yamma waɗanda ke ƙoƙarin kwasar albarkatun ƙasar.

A ƙasar, mutane ƙadan ne kawai suka fuskance shi, amma wasu da suka yi ƙoƙarin zaƙe masa sun sha baƙar wuya.

Duk abin da shugaban ya ce ta zauna, kusan kowane lokaci, in ji Zitto Kabwe, wanda shugaban ‘yan adawa ne a ƙasar wanda aka kama fiye da sau 12 tun 2016.

“Ƙasar na so mu yi shiru, suna yi mana barazana. Babban makami garemu shi ne mu yi magana mu ƙara tayar da ƙura,” a tattaunawarsa da kamfanin dillancin labarai na AP a watan Yuli.

Babban ɗan adawa a zaɓen ƙasar mai zuwa shi ne Tundu Lissu daga Jam’iyyar Chadema wanda ya tsira daga yunƙurin kashesa a 2017, inda ya buƙaci zama na kusan shekara uku a ƙasar waje domin duba lafiyarsa.

Babu wanda aka kama da laifin yunƙurin kisan nasa, kuma babu wasu bayanai daga ‘yan sandan ƙasar kan wannan lamarin.

A ‘yan makonnin da suka gabata, hukumar zaɓen ƙasar ta haramta masa yaƙin neman zaɓe na kwanaki bakwai inda take zarginsa da da saɓa ƙa’idojin yaƙin neman zaɓen musamman kan kalaman da ya yi ga shugaban ƙasar.

A daidai lokacin da zaɓen ƙasar ke matsowa kusa, Magafuli na da damar samun sa’ar zarcewa sakamakon goyon bayan da yake samu daga jam’iyyar da ba ta taɓa faɗuwa zaɓe a ƙasar ba.

Ɗan takarar ‘yan adawa Tundu Lissu ya yi alƙawarin ƙara haɓaka tattalin arziƙin ƙasar da kuma mutunta haƙƙin ɗan adam. Sauran manyan ‘yan adawan sun haɗa da Bernard Membe, wani tsohon minista wanda ya fito takara ƙarƙashin Jam’iyyar ACT-Wazalendo.

Idan Magafuli ya ci zaɓe a karo na biyu, ya yi alƙwarin ci gaba da gudanar da ayyukan ci gaba da kuma taimaka wa rayuwar mutane.

Amma sai dai idan yanayin gudanar da mulkinsa ya sauya, wasu daga cikin ‘yan adawa da kuma ‘yan jarida masu zaman kansu na nuna fargabarsu kan makomar ƙasar a nan gaba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here