Tinubu ya Bada Gudunmuwan N50m ga  Wadanda Sukayi Asarar Dukiya a Gobarar Babbar kasuwar Jahar Katsina

 

Babban jagora a jam’iyyar All Progressives Congress (APC) kuma tsohon gwamnan jahar Legas, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya bada gudunmuwan miliyan 50 ga wadanda sukayi asarar dukiya a gobarar babbar kasuwar jahar Katsina.

Channles TV ta rahoto cewa Tinubu ya sanar da hakan ne ranar Laraba yayinda ya kai ziyarar jaje ga gwamnatin jahar Katsina.

Gwamnan jahar Katsina, Aminu Bello Masari, da wasu manyan jami’an gwamnatin jahar suka tarbe shi.

Kasuwar jahar Katsina ta ci bal-bal ne ranar Litinin inda akayi asarar dukiya na miliyoyin naira.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here