Shugaba Tinubu da Mataimakinsa za su Fara Biyan Haraji a Filin Jirgin Sama
Yayin da ake korafe-korafen kan ƙaƙaba haraji da gwamnatin Bola Tinubu ke yi, shugaban bai ware kansa ba a lamarin.
Tinubu ya soke dokar da ta hana shi da mataimakinsa, Kashim Shettima biyan harajin a filayen jiragen saman kasar yayin shiga.
A zaman majalisar zartarwa a yau Talata 14 ga watan Mayu, an tabbatar da cewa Tinubu da Kashim za su fara biyan kudin fakin a filin jirgi.
FCT, Abuja – Shugaba Bola Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima ba su tsira daga biyan haraji ba a Najeriya.
Read Also:
Tinubu da Shettima za su biya kudin fakin a dukkan filayen jiragen sama a Najeriya kamar yadda kowa ke biya.
Dokar ta aka ƙaƙaba kan Tinubu, Shettima
Wannan ya biyo bayan zaman majalisar zartarwa kan kin biyan haraji da wasu manyan jami’an gwamnati ke yi a filayen jiragen sama, cewar Punch.
Ministan harkokin jiragen sama, Festus Keyamo shi ya bayyana haka a yau Talata 14 ga watan Mayu yayin ganawa da manema labarai.
Keyamo ya ce Najeriya na asarar akalla 82% na kudaden shiga da ake samu yayin shiga filayen jiragen saman kasar.
Tun farko dokar ta ware shugaban kasa da mataimakinsa amma Bola Tinubu ya soke wannan doka daga yau.
Tinubu ya ce da shi da mataimakinsa, Kashim Shettima da sauran hadimansu za su ci gaba da biyan wadannan kudi.
Karin bayani na tafe….