kokarin Toshe Bakin Jama’a ba Zai Tabbata ba – IBB ga Gwamnati Mai ci

 

Tsohon shugaban kasan Najeriya na mulkin soji, Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya ce duk kokarin rufe bakin jama’a ta kafar sada zumunta ba zai tabbata ba.

Dama an dade ana zargin wannan mulkin sun yi iyakar kokarin ganin sun toshe bakin jama’a, duk da dai gwamnati ta dade tana musa wannan zargin.

A wata tattaunawa da aka yi da IBB a ranar Juma’a a Minna, babban birnin jahar Neja, ya ce ‘yan Najeriya ba zasu taba barin hakan ya faru ba

Minna, Niger – Tsohon shugaban kasan Najeriya na mulkin soji, Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya ce duk wani kokarin toshe bakin jama’a ba zai tabbata ba.

Wannan mulkin yayi kokarin tsuke bakin jama’a tuntuni, duk da dai gwamnati ta dade tana musa wannan zargin.

Amma a wata tattaunawa da ARISE TV tayi IBB a gidansa dake hilltop a Minna, jahar Neja a ranar Juma’a, ya ce ‘yan Najeriya ba zasu taba barin hakan ya yuwi ba don zasu jajirce kwarai.

Kokarin rufe bakin jama’a ba zai taba yuwuwa ba. Jama’a ba zasu taba barin hakan ya tabbata ba.

Shirme ne kace zaka rufe bakin jama’a saboda kafafen sada zumunta ita ce kadai hanyar da jama’a suke da ita ta bayyana damuwarsu don haka abar su su yi yadda sukeso, a cewarsa.

IBB ya jinjinawa kokarin ‘yan Najeriya

Ya nuna jin dadinsu akan jajircewar ‘yan Najeriyata yadda suka ki bari shugabanninsu su rufe musu bakunansu.

Tsohon shugaban kasar ya ce ‘yan Najeriya ba zasu taba tsayawa a wuri daya ba, jajircewar ‘yan Najeriya ne zai bunkasa kasar ta dawo hayyacinta.

‘Yan Najeriya ba zasu bari su zama ‘yan jam’iyya daya ba. Za suyi magana, su yi nuni sannan su yi duk abinda sukeso ba tare da wani ya hanasu ba.

Mene ne babbar matsalar Najeriya? IBB ya bayyana babbar matsalar Najeriya a matsayin zaluncin masu mulki amma su yi ta cewa rashin tsaro ne.

Akwai rashin jituwa tsakanin shugabanni da mabiyansu. Ya kamata shugabanni su fahimci Najeriya da ‘yan Najeriya sannan yakamata su dinga yin abubuwa don cigaban jama’a.

Sannan ya kara baiwa ‘yan Najeriya kwarin guiwa da cewa har yanzu Najeriya bata gama lalacewa ba. Shugabanni zasu iya farfado da ita.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here