IBB ya Bayyana Dalilin da Yasa Ake Masa Laƙabi na Mugun Gwani da Maradona

Ibrahim Badamasi Babangida (IBB), tsohon shugaban kasa, ya yi karin haske kan yadda ya samu laƙabi na mugun gwani da Maradona.

Tsohon shugaban kasar na mulkin soja a ranar Juma’a, 6 ga watan Agusta, a wata hira da gidan talabijin na Arise yace kafafen yada labarai ne suka samar da sunayen.

A cewarsa, an kira shi Maradona ne saboda dabarun siyasa.

Tsohon shugaban kasar Najeriya a mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida (IBB) ya bayyana yadda aka yi masa lakabi da “evil genius” wato “mugun gwani” da “Maradona”.

Babangida, ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da Arise TV a wata hira da jaridar The Nation ta sa ido a ranar Juma’a, 6 ga watan Agusta.

Ya bayyana cewa kafafen yada labarai ne suka kakaba masa wannan sunan saboda “ƙaƙƙarfan salon siyasarsa”.

Babaginda ya ce:

“Wannan abu ne mai kyau game da kafofin watsa labarai na Najeriya da mutanen Najeriya, dole ne ka hange su.

“Idan ka hange su to sai ka zauna lafiya da su. Suna kirana da ‘mugun gwani’, ina mamakin hakan. Ba za ka iya kasancewa mugu ba sannan ka zama gwani.”

“Ma’anar Maradona da na samu daga kafafen yada labarai shine saboda dabarun siyasa. Wannan shine yadda kafofin watsa labarai suka bayyana shi.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here