Jahar Osun Sun Sanar da Ranar Litinin, 9 ga Agusta a Matsayin Ranar Hutun Shiga Sabuwar Shekarar Musulunci

Gwamnan jahar Osun, Gboyega Oyetola, ya sanar da ranar Litinin, 9 ga Agusta, a matsayin ranar hutu don murnar shiga sabuwar shekarar Musulunci – Hijrah 1443 AH.

Wannan na kunshe cikin jawabin da Kwamishanan harkokin cikin gidan jahar, Tajudeen Lawal, ranar Juma’a a Osogbo, rahoton NAN.

Gwamnan ya yi kira ga Musulmai da masu bin sauran addinai suyi amfani da hutun domin addu’a ga cigaban jahar da Najeriya gaba daya.

Ranar farkon sabuwar shekarar Hijra zai kama ranar Litinin ko Talata dangane da ranar da aka ga wata.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here