Malaman Addinai na Jahar Plateau Sun yi Alla-Wadai da Asarar Rayuka da Dukiyoyi da Kai a Jahar

 

Rikici a Pleteau kwanakin baya ya yi sanadiyyar asarar rayuka da dukiya.

Gwamnatin Plateau ta ce an kwantan da kuran yanzu bayan kwanaki hudu.

Malaman addinai na jahar sun yi Allah-wadai da wannan kashe-kashe.

Majalisar Malaman addinai a jahar Plateau ta yi Alla-wadai da kashe-kashe da asarar gonaki, gidaje da sauran dukiyoyi dake faruwa a wasu sassan jahar kwanakin nan.

Majalisar a jawabin da ta saki ranar Juma’a a Jos kuma shugabanninta Pandang Yamsat da Muhammadu Haruna, suka rattafa hannu, sunce wannan kashe-kashe ya saba dokokin Allah, rahoton DN.

Yamset Pandang shine tsohon shugaban cocin COCIN, yayinda Mohammadu Haruna shine Sarkin Wase kuma shugaban kungiyar Jama’atu Nasril Islam, JNI, a jahar.

A cewar majalisar, wannan abu dake faruwa ya sabawa koyarwan addinin Musulunci da na Kirista.

Jawabinsu yace:

“Majalisar IRC wacce ta kunshi shugabannin Kirista da Musulunci a jahar Plateau sun yi Alla-wadai da bayyana fushinsu kan kashe-kashe, kone-konen gidaje da gonaki dake faruwa a Bassa, Riyon da Barkin Ladi.”

“Wannan kashe-kashe gaba daya sun sabawa dokokin addinin Musulunci da Kirista; sun sabawa dokokin Allah kuma rashin tausayi ne.

Kuma hakan na da hadari ga rayuka, abinci da tattalin arzikin jahar da kasar ga baki daya.”

“A matsayinmu na Malaman addini, muna kira ga dukkan wadanda ke da hannu cikin wannan abu su sauya tunani kuma su tattauna da juna kamar da littafai addinai suka koyar.”

Majalisar ta yi kira da gwamnati da jami’an tsaro su tsaurara matakan tsaro domin kawo karshen matsalar a jahar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here