Ukraine ta Bayyana Cewa Babu Wani Tsari na Kwashe Fararen-Hula Daga Kasar a Yau
Mataimakiyar firaiministan Ukraine ta ce babu wani shiri na bude kafofin ficewa daga kasar domin kwashe fararen-hular da suka makale a biranen kasar a yau.
Read Also:
Iryna Vereshchuk ta ce an dauki matakin ne saboda bayanan sirrin da aka samu cewa akwai yiwuwar Rasha za ta iya tare hanyoyin.
Ta ce san samar da kafofin ficewa marasa hadari a Mariupol da Sumy kuma garuruwa da kauyukan wajen Kyiv wanda a yanzu dakarun Rasha suka kusan kewaye shi.
Lugudan wutar da Rasha ta yi a baya sun hana kwashe fararen-hula daga biranen da aka yi wa kawanya.