Gwamna Umahi ya Maida wa Fani-Kayode Martani Kan Kalaman da ya yi Bayan Komawarsa APC
David Umahi ya maida martani a kan wasu kalamai da Femi Fani-Kayode ya yi jiya.
An ji Fani-Kayode yana cewa ya taimaka wajen karkato da ra’ayin gwamnonin PDP.
Umahi yace Fani-Kayode bai san lokacin da ya zabi ya sauya-sheka zuwa APC ba.
Ebonyi – Gwamna David Umahi na jahar Ebonyi ya bukaci Femi Fani Kayode ya janye kalaman da ya yi bayan sauya-shekarsa zuwa jam’iyyar APC a jiya.
An rahoto tsohon Ministan harkokin jirgin sama, Cif Femi Fani Kayode yana cewa ya taka rawar gani wajen jawo wasu gwamnoni daga PDP zuwa APC.
Jaridar Daily Trust ta rahoto daya daga cikin sababbin shiga jam’iyyar APC yana maida martani, inda yace ya kamata Fani-Kayode ya janye kalamansa.
Ka janye kalaman ka, karya ne – Umahi
Read Also:
“Ina tunanin ya kamata ya janye kalamansa, aboki na ne, amma rainin hankali a wurina da sauran gwamnoni.”
“Mutumin nan bai san lokacin da na sauya-sheka ba, ya kawo mani ziyara, kuma yace shi ma zai shigo (jam’iyyar APC) tare da mu da sauran gwamnoni.”
Dave Umahi yace a matsayinsa na shugaban gwamnonin jahohin kudu maso gabashin Najeriya, Fani-Kayode bai da ta-cewa a kan matakin da zai dauka.
“Ya za ayi wanda yake jam’iyyar PDP ya taka rawar gani wajen sauya-sheka ta. Gwamna guda! Ba karamin gwamna ba fa, gwamnan da ya kware a aiki.”
“Dole ya lashe amansa. Bai cikin wadanda aka zauna da su lokacin da zan tashi. Na bar kudu maso gabas, na hade da gwamnatin tarayya da ke kan mulki.”
“Wani ya zo yana cewa ya yi kokari wajen tafiya ta, ina shugaban gwamnonin kudu maso gabas, kamar rainin hankali ne a wuri na. Ya janye kalamansa.”
Punch tace Gwamnonin da suka bar PDP zuwa APC bayan Dave Umahi su ne; Ben Ayade da Bello Matawalle.