Budaddiyar Wasika Zawa ga Gwamnatin Tarayyar Najeriya

 

Sunana Amb auwal muhd danlarabawa shugaban gidauniyar Tallafawa mabukata daga tushe na kasa wadda aka fi sani da Grassroot Care and Aid Foundation GCAF.

ina mai kira ga gwamnatin tarayyar najeriya karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu buhari wajen nemanwa matasa tallafi wanda zai anfane su kuma ya kara sanyaya zukatan matasan da karfafa musu  cewar gwamnatin tana sane dasu sannan tana son faranta zukatansu a wannan yanayi da ake ciki wanda aka dauki dogon lokaci ana zaune a gida ba makarantu.

kiran nawa dai shine gwamnatin tarayyar nejeriya ta fito da wani tsari wanda zai tallafawa daliban dake karatu a makarantun gaba da sakandiri ta hanyar neman alkalumansu nasu daga makarantun da suke karatu ta lambobin rijistar su na zama dalibai abi kowanne a bashi tallafin da zai taimaka musu a harkokin rayuwar su dama bangaren neman ilimin nasu.

wannan tallafi zaiyi matukar anfani kuma zai kara musu soyayyar kasa da gwamnatin baki daya sannan zai zama wani banagare na kara samar da zaman lafiya a kasa gefe guda kuma zai rage radadin talaucin da aka tsinci kai a sakamakon cutar covid-19 data dagula al’amuran daliban da jefa su cikin bacin rai na kasa cimma nasarar da suka saka a gaba fannin karatun nasu akan lokacin da suka tsammanin kammalawa.

ina fatan gwamnatin tarayyar najeriya zata duba wannan shawara tawa dan tallafawa daliban kasar nan a matatin tallafin covid-19 da zai rage radadin kuncin da dalibai ke ciki dan kar a cigaba da anfani da wasu daga ciki ana basu wasu yan kudade dan su tada mana hargitsi a kasa.

Nagode

Allah ya taimaki kasar mu najeriya ya bamu zaman lafiya da cigaban tattalin arziki.

Amb Auwal Muhd Danlarabawa Grassroot Care & Aid Foundation #08060257925 kano,Nigeria#[email protected]

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here