Najeriya: Wasu Sabbin Mutane Sun Kamu da Cutar Korona

Maimakon samun sauki, daruruwan yan Najeriya na sake kamuwa da cutar Korona.

Gwamnatin tarayya na tsoron adadin masu kamuwa da cutar zai yi tashin gwauron zabi sakamakon zanga-zangar ENDSARS.

Hukumar NCDC ta tsara shirin yadda maus bautan kasa NYSC zasu shiga sansani a fadin tarayya Najeriya ta samu adadin sabbin masu cutar Coronavirus 223 ranar Juma’a a cewar hukumomin kiwon lafiya.

Adadin da aka samu ranar Laraba ya kai jimillan wadanda suka kamu da cutar 63,731 a Najeriya.

Hukumar hana yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta sanar da hakan a daren Juma’a , 6 ga watan Nuwamba, 2020. Yayinda adadin masu kamuwa ke raguwa, adadin masu samun waraka daga cutar na kara yawa.

Daga cikin mutane sama da 63,000 da suka kamu, an sallami 59,844 yayinda 1154 suka rigamu gidan gaskiya.

Jerin jihohi da Sabbin mutanen da suka kamu: Lagos-85, FCT-35, Akwa Ibom-24, Enugu-18 Plateau-13, Rivers-10 , Abia-7 , Ebonyi-6, Anambra-5, Adamawa-4 , Bauchi-3, Imo-3, Ogun-3, Oyo-3 , Kwara-2, Osun-1, Taraba-1

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here