Ali Kwara: Buhari ya yi Ta’aziyyar Rasuwar Jarumin

 

Kwara ya rasu ne a Abuja bayan fama da jinya kamar yadda majiya daga iyalansa suka sanar.

Shugaba Buhari ya mika ta’aziya ga gwamnati da al’ummar Bauchi inda ya yi addu’ar Allah saka wa Ali Kwara da Aljannah Shugaba Muhammadu Buhari a daren ranar Juma’a ya ce ba za manta da gudunmuwar da jarumin mafarucin, shugaban ‘yan banga kuma mai yaki da masu laifi ya bada ba wurin ‘dakile masu laifi da masu tada kayar baya a cikin daji ba.’

Shugaba Buhari, cikin sakon da kakakinsa Garba Shehu ya fitar ya yi alhinin rasuwar jarumin da ya bada gudunmawa wurin yaki da masu laifi.

“Jarumtar da mafaraucin ya yi wurin taka wa ‘yan bindiga, ‘yan fashi da’yan ta’adda birki a kusan dukkan jihohin arewa 19 ba boyeyyen abu bane, gwamnati ta kawo shi Abuja ne don cigaba da kula da jinyarsa,” a cewar sanarwar.

Ya ce fadar shugaban kasa a daren ranar Alhamis ta bada jirgin sama da zai kai gawar mammacin zuwa filin tashin jirage na Dutse inda daga nan za a tafi da shi garinsa na Azare a Jihar Bauchi inda za a yi masa jana’iza.

“A madadin gwamnati da dukkan mutanen kasa, ina mika ta’aziyya ga gwamnatin Bauchi da al’ummar jihar bisa rasa wannan jarumin da ya sadaukar da rayuwarsa don taimakawa jami’an tsaro yaki da bata gari.”

“Ba za a manta da rawar da Ali Kwara ya taka ba wurin dakile shu’uman masu laifi a dazuka.

Muna godiya da kokarinsa, da yawa cikin masu laifin sun tuba inda wasu da dama suka fuskanci hukunci.

Samun jarumai irinsa abu ne mai wuya a wannan zamanin. Allah ya saka masa da gidan Aljannah,” a cewar sanarwar

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here