Ibadan: Babban Shagon Uwar Gidan Ajimobi ya Kama da Wuta

Babban kantin uwar gidan Ajimobi ya kama da wuta a Ibadan.

A yanzu haka yan kwana-kwana na nan suna kokarin ganin sun kashe gobarar wacce ba a san musabbabinta ba.

Har ila yau an girke jami’an tsaro domin hana bata gari amfani da damar wajen yin sace-sace Wani bangare na kantin Bodija da ke babban kantin Grandez mallakar uwar gidan tsohon gwamnan jihar Oyo, marigayi Abiola Ajimobi na nan yana ci da wuta.

Gobarar wacce ta fara daga bayan ofishin da ke kantin, na nan yana yaduwa a hankali zuwa aihanin manyan kantunan, jaridar The Nation ta ruwaito.

Jami’an hukumar kashe gobara ta jihar Oyo, wadanda suka isa wajen a kan lokacci na nan suna gwagwarmayan hana wutar lakume dukkan kantin da kuma hana shi yaduwa zuwa gine-ginen da ke kusa.

An kuma gano jami’an tsaro na hadin gwiwa a wajen domin hana bata gari yin sata yayinda yan kwana-kwana ke kokarin kashe gobarar.

Bayan samun labari, Misis Ajimobi ta isa wajen tare da rakiyar wasu yan uwa da abokan arziki domin kula da halin da ake ciki.

Ba a san abunda ya haddasa gobarar ba a daidai lokacin kawo wannan rahoton. Duk da kokarin da yan kwana-kwana ke yi, gobarar na ci gaba da ci a daidai wannan lokacin.

Sannan kuma an fara samun cunkoson ababen hawa a yankin.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here