‘Yan Bindiga Sun yi Garkuwa da Amurkawa 15 a Haiti
Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wani rukunin ma’aikatan addinin Kirista na sa-kai kuma Amurkawa a ƙasar Haiti, waɗanda suka haɗa da iyalansu ciki har da yara.
Mutum 15 aka sace a kusa da babban birnin ƙasar, Port-au-Prince.
Read Also:
Babu wani cikakken bayani game da garkuwa da mutanen zuwa yanzu amma mahukunta a Amurkar sun ce suna sane da lamarin.
Haiti na ɗaya daga cikin ƙasashen da aka fi aikata garkuwa da mutane a duniya, yayin da ‘yan bindiga ke amfani da rikicin siyasa da rashin tsaro don neman kuɗin fansa.
Tun bayan kashe Shugaban Ƙasa Jovenel Moïse a watan Yuli, masu ɗauke da makamai da ke adawa da juna ke yunƙurin karɓe iko, abin da ke ƙara ta’azzara tsananin rayuwa da ‘yan ƙasar ke ciki.