Karbar Kudin Fansa: Yan Banga Sun Harbe Mai Garkuwa da Mutane a Jahar Adamawa

 

Rundunar ‘yan sandan jahar Adamawa sun sanar da yadda ‘yan banga suka bindige mai garkuwa da mutane yayin karbar kudin fansa.

Miyagun sun kutsa wani gida a yankin Balms da ke Song inda suka kashe maigidan tare da sace diyarsa mai suna Queen Bakomi.

A yayin kai musu kudin fansa ne ‘yan banga suka yi kwanto sannan suka bude musu wuta tare da kashe daya da kuma ceton Queen.

Song, Adamawa – ‘Yan sandan jahar Adamawa sun tabbatar da sheke wani mai garkuwa da mutane da ‘yan banga suka yi yayin da ya je karbar kudin fansa daga ‘yan uwan wacce ya sace, Daily Nigerian ta rawaito.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jahar, DSP Sulaiman Nguroje, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin ga Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a ranar Laraba a Yola, ya ce lamarin ya faru a ranar 26 ga watan Augusta a karamar hukumar Song ta jahar.

Rundunar ‘yan sandan jahar ta samu rahoto daga ‘yan sandan Song a ranar 26 ga watan Augusta kan cewa ‘yan banga sun sheke wani da ake zargi da garkuwa da mutane yayin karbar kudin fansa,” Nguroje ya ce.

Ya ce rundunar ta na bincike kan lamarin amma majiya mai karfi kuma dan banga a kauyen Murke, ya sanar da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya cewa, a ranar 20 ga watan Augusta ne miyagu suka kutsa yankin Balms.

Daily Nigerian ta rawaito cewa, Majiyar ta ce yayin harin, miyagun sun kutsa gidan wani Bakomi Andrawus inda suka bindige shi kuma ya mutu a take.

Bayan kashe Bakomi Andarawus, masu garkuwa da mutanen sun sace diyarsa, Queen Bakomi.

Ta kwashe kwanaki shida a wurinsu kuma sun bukaci karbar naira miliyan biyu a matsayin kudin fansa kafin su sake ta.

Yayin da iyalan mamacin suke kokarin birne shi, sun tattara kudi har N170,000 domin karbo ta,” majiyar tace inda ta kara da cewa sun roki masu garkuwa da mutanen kuma sun amince da su kai kudin haka.

Ya ce masu garkuwa da mutanen sun umarci wakilan wacce suka sace da ya kai kudi wani daji inda za su karba.

Ganin tashin hankalin da iyalan ke ciki, ‘yan banga sun yanke hukuncin tunkarar masu garkuwa da mutanen. Sun yi kwanto a dajin wurin karfe 8:30 na dare kafin masu karbar kudin su iso,” yace.

Ya ce ‘yan bangan sun budewa miyagun wuta inda suka kashe daya yayin da suka kubutar da wacce aka sace cike da nasara.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here