Datse Layukan Sadarwa: ‘Yan Bindiga Sun Koma Amfani da Kafofin Sadarwa na Kasashe da ke Makwabtaka da Najeriya – ‘Dan Majalisar Sokoto
Dan majalisar jahar Sokoto ya ce ‘yan bindiga sun koma amfani da layikan sadarwan Nijar wurin kai farmaki.
Aminu Almustapha Gobir ya ce hatta shi da kanshi ya samu barazanar ‘yan bindiga cewa za su kai masa da yankinsa farmaki a Sokoto.
Ya sanar da cewa miyagun sun kai farmaki sansanin soji da ke Dama a karamar hukumar Sabon Birni har sun sheke sojoji 12.
Sokoto – ‘Yan bindiga suna yin amfani da kafofin sadarwa na jamhuriyar Nijar wurin kai farmaki kamar yadda Aminu Almustapha Gobir, dan majalisa mai wakiltar mazabar Sabon Birni ta arewa a majalisar jahar Sokoto.
Daily Trust ta rawaito cewa, daga cikin hanyoyin magance matsalolin ‘yan fashin bindiga, gwamnatin Najeriya ta datse dukkan hanyoyin sadarwa a jahohin Sokoto, Zamfara da Katsina.
Hakan an gano cewa ya datse sadarwa tsakanin ‘yan bindigan da masu kai musu bayanai.
Amma a matsayin hanyar cigaba da aiwata ta’asa, ‘yan fashin sun koma amfani da kafofin sadarwa na kasashe da ke makwabtaka da ke da Najeriya ta Sokoto.
Read Also:
Gobir ya ce shi da kan shi ya samu barazana daga wani dan bindiga da ke amfani da layin sadarwa na kasar Nijar.
“Dan fashin dajin ya na min barazanar cewa zai jagoranci tawagar sa domin su kawo min farmaki da yanki na,” ya sanar da Daily Trust.
Gobir ya kara da tabbatar da farmakin da ‘yan fashin suka kai sansanin sojoji da ke karamar hukumar Sabon Birnin ta jahar.
Daily Trust ta rawaito yadda wasu ‘yan bindiga suka kai samame sansanin sojoji inda suka kashe jami’in tsaro tare da banka wa tankar fetur wuta.
“Da gaske ne sun kai farmaki sansanin sojoji da ke Dama kumaa sun kashe 12 daga ciki yayin da wasu suka bace har yanzu.
“A saboda haka ne na ke ganin laifin gwamnati da ta rufe layikan sadarwa a yankin gabashin jihar ba tare da bada sojoji isassu domin mamaye wurin ba.
“’Yan fashin dajin na amfani da layikan sadarwa na Nijar domin sadarwa a tsakaninsu tare da aiwatar da miyagun ayyukansu.
“Na yi tsammanin gwamna zai samarwa ‘yan sanda da sojoji wayar Thuraya wacce za ta basu damar sadarwa tsakaninsu da manyansu idan suna bukatar taimako inda babu layikan.
“Hakan gwamnan Zamfara yayi kuma tabbas kwalliya ta na biyan kudin sabulu,” yace.