Harin ‘Yan Bindiga a Barikin Sojojin Jahar Sokoto ya yi Sanadiyyar Hallaka Mutane da Dama 

 

Wasu miyagun yan bindiga sun kai hari barikin sojoji a jahar Sokoto, inda suka hallaka jami’ai dama.

Rahotanni sun tabbatar da cewa maharan sun kai harin ne da safiyar Jumu’a, kuma an nemi wasu sojoji da dama an rasa bayan harin.

Wani jami’in hukumar NSCDC, ya bayyana cewa daga cikin waɗanda aka kashe a harin harda abokan aikinsa guda uku.

Sokoto – Tsagerun yan bindiga sun kai hari sansanin sojoji a ƙaramar hukumar Sabon Gari, jahar Sokoto, inda suka kashe jami’ai da dama.

Wakilin Dailytrust ya gano cewa barikin sojojin dake a Kauyen Dama, an laƙaba masa suna, “Sansanin Burkusuma.”

Wata majiya ta bayyana cewa maharan sun kai hari sansanin sojojin ne da sanyin safiyar ranar Jumu’a da ta gabata.

Tsohon shugaban karamar hukumar Sabon Gari, Idris Muhammad Gobir, ya shaidawa wani mutumi mai suna Ɗanchaɗi, wanda ya tabbatar da kai harin.

Sojoji nawa maharan suka kashe?

Mutumin ya bayyana cewa maharan sun hallaka mutane da dama, sannan kuma an nemi wasu jami’an sojoji an rasa bayan harin.

Bugu da ƙari tsagerun sun ƙone motoci guda biyu, sannan suka yi awon gaba da wata guda ɗaya, wacce suka yi amfani da ita wajen jigilar kayan abinci da suka sace a ƙauyen.

Wani sanannen basarake a yankin da lamarin ya faru, ya bayyana cewa an tura motoci barikin domin ɗakko gawarwakin dakarun sojojin da suka mutu a harin.

Basaraken yace “Motocin sojoji sama da 10 sun bazama cikin jeji domin nemo maharan da kuma ɗaukar fansa kansu.”

Wane mataki jami’an tsaro suka ɗauka?

Wani jami’in hukumar tsaro ta NSCDC wanda ya nemi a sakaya sunan shi, ya tabbatarwa wakilim Dailytrust cewa akwai jami’an hukumarsu uku da harin ya ritsa da su.

ajiyar gawarwaki domin ɗakko gawar su, a yi musu jana’iza.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here