Afghanistan: Taliban ta Haramta Aske Gemu da Kuma Kunna kiɗa

 

Hukumomin Taliban a Lashkar Gah a lardin Helmand na Afghanistan sun haramta aske gemu da kuma kunna kiɗa.

Hukumomin na Taliban sun sanar da ɗaukar matakin ne bayan ganawa da masu aski.

A cikin wata sanarwa, Taliban ta ce duk wanda ya saɓa dokar zai fuskanci hukuncin da “dokokin addini suka tanadar.”

Masu aski kuma sun ce Taliban ta kuma hana yi wa mutane aski irin na zamani.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here