‘Yan Bindiga Sunyi Garkuwa da Abokan Ango a Jahar Taraba
Wasu ‘yan bindiga sun yi awun gaba da wasu matasa 25 dake kan hanyarsu ta dawowa daga daurin aure.
Majiya ta bayyana cewa matasan sun fada shingen ‘yan fashin ne a hanyarsu ta dawowa daga Wukari.
Kakakin rundunar jihar Taraba ya tabbatar da faruwar hakan yayin da ya bayyana ba asan halin da suke ciki ba.
Wasu ‘yan bindiga wadanda ake zargin masu satar mutane ne sun sace wasu matasa 25 a kan hanyar Wukari zuwa Takum da karfe 6 na yammacin Laraba.
Wata majiya mai tushe a Wukari da Takum ta shaida wa Daily Trust cewa matasan 25 na kan hanyarsu ta komawa Takum ne daga Wukari inda suka halarci bikin aure a lokacin da suka yi karo da shingen kan hanya da ’yan bindiga da ake zargin masu satar mutane suka yi.
Wadanda lamarin ya rutsa da su duka maza ne, kamar yadda Daily Trust ta gano.
Read Also:
Suna tafiya ne a cikin motar bas ta kasuwanci sai suka ci karo da shingen a wani wuri da ke tsakanin Kofar Amadu da Chanchangi kafin ‘yan bindigar su karkaratar da motar ta shiga daji.
Wani dan uwan wasu daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su, Malam Muhammed Takum, ya shaida wa Daily Trust a wata tattaunawa ta Wayar tarho cewa wadanda lamarin ya rutsa da su sun halarci bikin daurin auren wani abokinsu a Wukari.
Ya kuma tabbatar da an sace su ne a lokacin da suke kan hanyarsu ta komawa Takum.
Muhammed ya ci gaba da cewa har zuwa yanzu masu garkuwan ba su tuntubi iyalan wadanda abin ya shafa ba.
Ya ce akwai tashin hankali a garin saboda babu wanda ya san inda matasan suke, ciki har da direban motar bas din da ya kai su.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Taraba, DSP David Misal, ya tabbatar da faruwar lamarin.
“Mun tabbatar da cewa sun bata amma ba a tabbatar ko an sace su ko kuma akasin haka ba. “An fara bincike,” in ji DSP Misal.