‘Yan Bindiga Sunyi Garkuwa da Wasu ‘Yan Gida ɗaya
Ana cigaba da samun ƙaruwar matsalar garkuwa da mutane a yankin Arewacin Najeriya.
Wasu ƴan bindiga sun yi awon gaba da ƴan gida ɗaya su biyar a Pegi da ke babban birnin tarayya Abuja.
Ƴan bindigan sun bi su har gidansu misalin ƙarfe 11 na daren Litinin 16 ga watan Nuwamba suka tisa ƙeyarsu Wani rahoton da Daily Trust ta wallafa ya nuna cewa an sace wasu ƴan gida ɗaya su biyar a garin Pegi da ke ƙaramar hukumar Kuje a Abuja.
A cewar rahoton, wadanda aka yi garkuwa da su sun hada da Jubril Abdullateef (22), Sherifat Abdullateef (20), Muyidat Abdullateef (13) Nura Abdullahi (18) da Nahimat Abdullahi (9).
Read Also:
Ƴan bindigan sun afka gidansu misalin ƙarfe 11 na daren ranar Litinin 16 ga watan Nuwamba inda suka sace su a cewar rahoton.
Wani maƙwabcinsu ya ce; “Mahaifinsu baya gida don ya tafi gidan ɗayan matarsa ya kwana a lokacin da ƴan bindigan suka afka gidan.
“Ƴan bindigan sun kwace wayar mahaifiyarsu suka umurce ta da yaranta su fita waje a lokacin da tayi yunkurin kirar mai gidan.”
Ya ce ƴan bindigan sun kwace kimanin minti 20 ba tare da yin karbi ba sannan suka tsere da yaran kafin ƴan sanda da sojojin ruwa da ke kusa da unguwar su iso.
Kakakin kungiyar cigaban Pegi, Oyedeji Oyetunji ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya ce; “Abinda muke fuskanta a Pegi shine wasu ƴan bindiga sun shiga gidan maƙwabtan mu sun sace ƴan gida ɗaya su biyar.”
Da aka tuntube shi, Kakakin ƴan sandan Abuja, ASP Mariam Yusuf ta ce, “Ka ɗan dakata, za mu fitar da sanarwa game da afkuwar lamarin.”