Majalisar Dattawa ta Fadi Ranar Karshen Kasafin Kudin 2021

Kwamitin majalisar dattawa kan lissafe-lissafen kasafin kudi a ranar Laraba ta yi alkawatin gabatar da kammalallen daftarin kasafin 2021 a zauren majalisa ranar 3 ga Disamba.

Shugaban kwamitin, Sanata Barau Jibrin, ya bayyana hakan bayan shugabannin wasu kwamitoci suka gabatar da rahotanninsu.

Barau ya bayyanawa yan jarida cewa bayan gabatar da kasafin a zauren majalisar, Sanatocin zasu gaggauta amincewa da ita, The Punch ta ruwaito.

Yace: “Muna da jadawalinmu; muna son gabatar nan zuwa ranar 3 ga Disamba, 2020. Zamu gabatar da daftarin kasafin kudin 2021 idan Allah ya yarda.”

Yayinda aka tambayeshi shine kwamitin za tayi tsokaci kan cire wasu ma’aikatu daga cikin kasafin, shugaban kwamitin yace duka wannan ba matsala bane.

Ya ce kwamitin za ta magance duk wani matsala.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here