Kotu ta Yanke Wa Wani Matashi Hukuncin Kisa

Kotu a Jihar Adamawa ta yanke wa wani mutum hukuncin kisa ta hanyar rataya don samunsa da laifin kashe ɗansa.

Bincike ya tabbatar da cewa mutum ya kashe ɗansa kuma ya fille kansa da nufin samun Naira miliyan ɗaya.

Wanda ake yanke wa hukuncin ya ce wani Alhaji Hassan ne yace masa zai bashi N1m idan ya kawo ƙan ɗan adam.

Wata kotu da ke zamanta a Yola Adamawa, a ranar 18 ga watan Nuwamba ta yanke wa wani makiyayi, Bappa Alti hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda kashe ɗan cikinsa don Naira miliyan ɗaya.

Babban Kotun Jihar ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Fatima Ahmed Tafida ta samu Bappa da laifin kashe ɗansa ta hanyar bugunsa da sanda a kai daga bisani ya datse kansa da adda.

Wanda ake yanke wa hukuncin yana da shekaru 24 a lokacin da abin ya faru ya tafi da ɗansa, Buba, gona a ranar 14 ga watan Yulin 2013 a Ganji da ke ƙaramar hukumar Gombi ta Jihar Adamawa ya datse kansa.

Alhaji Gyza, kakan wanda abin ya faru da shi ya tambayi inda jikansa ya ke sai Bappa ya faɗa masa ya bar shi a gona amma zai taho gida daga bisani.

Bayan an shafi kwanaki Buba bai dawo ba Alhaji Guza ya yi korafi a ofishin ƴan sanda a Gombi inda aka bazama neman jikansa.

Bayan an gano gawar Buba a ƙarƙashin wata bishiya an rufe da ganye, an kama Bappa kuma ya amsa cewa wani Alhaji Sange Hassan ya faɗa masa zai bashi Naira miliyan ɗaya indan ya kawo ƙan ɗan adam.

Ya amsa cewa ya aikata wannan mummunan aikin ne don ya samu kuɗin da zai tallafawa iyayensa, zargin da Alhaji Guza ya musunta.

Bayan amsa laifinsa da kuma nazarin hujjoji da suka haɗa da adar da aka yi kisar da ita kotu ta tabbatar da Bappa ne ya kashe ɗansa Buba kuma ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here