‘Ƴan bindiga sun Hallaka Mutum 21 a Sokoto
Rahotanni Sokoto da ke yankin arewa maso yammacin Najeriya sun ce akalla mutum 21 aka kashe a harin da ƴan bindiga suka kai a yankin Sabon Birni.
Ƴan bindiga sun buɗe wuta ne a lokacin da mutane ke cin kasuwar garin Unguwar lalle, kamar yadda mazauna yankin suka shaida wa BBC.
Sun kuma ce mutane da dama ne suka jikkata a harin, waɗanda ke kwance a asibitin garin Sabon Birni, wasu kuma an tafi da su zuwa Sokoto.
Rundunar ƴan sandan jahar ba ta fitar da sanarwa ba game da harin da kuma mutanen da aka kashe.
Amma tsohon shugaban karamar hukumar Sabon Birni, kuma yanzu ɗaya daga cikin mai ba gwamnan jahar Sokoto shawara Honarabul Abdullahi Mohammed Tsamaye ya tabbatar da harin na kasuwar Unguwar Lalle.
Ya ce ƴan bindigar sun ɓude wuta cikin kasuwar suna harbi kan mai uwa da wabi inda suka kashe mutane tare da ƙone motoci.
“A takaice mutum 21 aka kashe, wasu sun samu raunika da yawa suna kwance a asibitin sabon birni wasu kuma a Sokoto,” in ji shi.
 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here