Corona: Saudiyya ta Taƙaita Aikin Umrah ga Waɗanda Suka yi Rigakafin Cutar
Hukumomin Saudiyya sun sanar da taƙaita yawan masu aikin Umrah ga mutanen da kawai suka karɓi allurar rigakafin corona guda biyu.
Ma’aikatar kula da aikin Hajji da Umrah ta sanar da cewa sai waɗanda akwai aka yi wa rigakafin corona da gwamnatin Saudiyya ta amince da ita za a bari su yi aikin Umrah da kuma yin Ibadah a Masallacin Makkah da Madina, kamar yadda kamfanin dillacin labaran ƙasar na SPA ya rawaito.
Hakan na nufin dole sai mutum ya kammala karɓar allurar rigakafin corona guda biyu da ya kamata a yi wa mutum.
Saudiyya dai ta dakatar da aikin Umrah a watan Maris na bara daga cikin matakan da ta ɗauka na daƙile bazuwar corona kafin a buɗe daga baya.
An kuma rage yawan masu aikin hajji saboda annobar corona.
 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here