Sabon Hari: ‘Yan Bindiga Sun Hallaka Mutane 6 a ƙauyen ƙaramar Hukumar Tangaza Dake Sokoto

 

Wasu miyagun yan bindiga sun sake kai sabon hari ƙauyen ƙaramar hukumar Tangaza, inda suka hallaka mutum shida.

Rahotanni sun tabbatar da cewa miyagun maharan sun harbe mata biyu har Lahrira, sannan suka yanka wasu matasa huɗu.

Wannan harin yazo awanni ƙaɗan bayan wasu fusatattun mutane sun hallaka tare da ƙone gawarwakin yan bindiga 13 a garin Tangaza.

Sokoto – Yan bindiga sun kai sabon hari wani ƙauye a ƙaramar hukumar Tangaza, jahar Sokoto, inda suka hallaka mutum shida, kamar yadda Dailytrust ta rawaito.

Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun farmaki ƙauyen, wanda mafi yawancin mutanen cikinsa mafarauta ne, da sanyin safiyar ranar Lahadi.

Kuma yan bindigan sun kai harin ne dai-dai lokacin mafi yawan mazan garin sun fira sana’arsu ta farauta.

Shin harin yana da alaƙa da kashe yan bindiga 13?

Sai dai babu tabbacin cewa ko harin miyagun yana da alaƙa da kashe yan bindiga 13 da mutane suka yi, waɗanda suka kai hari garin Tangaza ranar Asabar.

Wata majiya ta shaidawa Dailytrust cewa wasu mata biyu na cikin waɗanda miyagun maharan suka hallaka a lokacin harin.

Yace: “Sun bindige mata guda biyu har Lahira, yayin da suka yanka matasa guda huɗu yayin mummunan harin.”

“Dukka yan bijilanti da kuma yan sa kai dake yankin sun bazama cikin daji domin neman waɗanda suka aikata wannan mummunan ta’addancin.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here