‘Yan Bindiga Sun Hallaka Sojoji 17 da Farar Hula 4 a Iyakar Mali, Burkina Faso da Nijar
Sojoji a ƙalla 17 ne da fararen hula huɗu aka kashe ranar Lahadi, sannan ba a ga wasu mutum tara ba, biyo bayan wani hari da ake zargin masu ikirarin jihadi ne suka kai.
Lamarin ya faru ne a garin Tessit da ke bakin iyakokin kasashe uku tsakanin Mali da Burkina Faso da Nijar, wajen da ake yawan samun hare-hare.
Wannan kiyasi na wadanda harin ya shafa na wucin gadi ne, kuma zai iya sauyawa, kamar yadda wata sanarwar rundunar sojin Mali a jiya Litinin ta ce..
Read Also:
Rundunar sojin ta kuma ce ta kashe mayaƙa bakwai da ake kyautata zaton ƴan ƙungiyar IS ne a yankin sahara, saboda taimakon da ta samu na amfani da jirgin mara matuƙi da kayan fashe-fashe da bama-bamai masu fasa motoci.
Sojin Malin ta kuma bayyana cewa sojoji 22 ne suka samu raunuka, sannan sun yi asarar motoci an kuma lalata shingayen tsaro.
Sannan a kalla wasu hare-hare biyu da mayakan sa kan suka kai sun yi sanadiyar rayukan fararen hula 12 ranar Asabar a tsakiyar Mali, da jami’an ƴan sanda biyar a ranar Lahadi a kudu maso yammacin kasar.
Kasar Mali na ci gaba da samun kalubalen ‘yan bindiga da ke ikirarin jihadi tun 2012, lamarin da a farko ya shafi arewacin kasar ne kadai.
Amma abun ya yaɗu zuwa tsakiya da kudancin Mali, da kuma makwabciya Burkina Faso da Nijar.