‘Yan Bindiga Sun Kashe ‘Dan Takarar Kansila a Kaduna

 

Jihar Kaduna – Wasu yan bindiga sun kashe dan takarar kansila a mazabar Pari, a karamar hukumar Kauru, a jihar Kaduna Raymond Timothy.

Shugaban karamar hukumar, Barnabas Chawai ne ya tabbatar da kisan, inda ya ce an kashe kansilan tare da kaninsa James Timothy.

A labarin da ya kebanta da Punch zuwa yanzu, an samu tabbacin yan bindiga sun kashe dan takarar kansilan da dan uwansa.

Lamarin ya faru ne suna kan babur a hanyarsu ta dawowa daga yakin neman zabe.

Ana zargin kisan siyasa a Kaduna Shugaban karamar hukumar Kauru a Kaduna, Barnabas Chawai ya yi zargin kisan dan takarar kansila a yankin, Raymond Timothy ba ya rasa nasaba da siyasa.

Marigayin dan takarar ya bar mace daya da yara uku, kuma matarsa na da juna biyu – ana sa ran za ta haifi na hudu a kwanan nan.

Kisan Kaduna: An nemi daukin yan sanda

An nemi yan sanda su gaggauta daukar mataki kan kisan dan takarar kansila a mazabar Pari da ke karamar hukumar Kauru a Kaduna.

Bayan zargin kisan na da alaka da siyasa, shugaban karamar hukumar, Hon. Chawai ya bukaci jami’an tsaro su sanya matakan dakile irin wannan kisan a gaba.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here