Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 6 a Jahar Katsina 

 

Yan bindiga sun kashe akalla mutum shida tare da garkuwa da wasu da dama a kauyen Unguwar Samanja na jahar katsina ranar Lahadi.

Kamar yadda jaridar Premium Times ta ambato wani mazauna kauyen Daudawa mai makwabtaka yana cewa, maharan sun isa kauyen kusan karfe shida na yamma, a lokacin da jama’a ke shirin sallar magariba.

Unguwar Samanja na karkashin karamar hukumar Faskari, wadda ta dade tana fuskantar hare-hare daga yan bindiga.

Kazalika tana daga cikin kananan hukumomi 13 da aka katse sadarwa, a wani bangare na yaki da yan bindiga.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here