Kuma Dai: ‘Ƴan cirani 140 Sun Nutse a Tekun Senegal

 

  Majalisar Dinkin Duniya ta tabbatar da mutuwar ‘yan cirani 140 da suka nutse a gaɓar tekun Senegal, bayan wani kwale-kwale da ya dauko su su 200 ya nutse.

An ceto mutum 60 a raye ya zuwa yanzu.

Kwale-kwalen sai da ya fara kamawa da wuta sannan ya nutse kuma.

Hukumar ta ce jirgin da ya kife a Senegal a cikin makon da ya gabata shi ne hadari mafi muni da aka taba yi a duniya a bana.

A cewar Hukumar kula da sufurin ruwa ta kasa da kasa, kimanin mutum 140 ne suka mutu lokacin da kwale-kwalen dauke da yan ci rani ya kama da wuta yan sa’oi bayan ya tashi ranar Asabar.

An yi kuma nasarar kubutar da kimanin mutum sittin sannan ana tunanin jirgin ya nufi tsibirin Canary ne.

Masu aiko da rahotanni sun ce a baya-bayan nan ana samun karuwar ‘yan cirani daga Yammacin Afirka da ke kokarin zuwa tsibirin wanda wani bangare ne na Spaniya.

Wannan hanya daga yankin Afirka ta yamma zuwa turai ta fara shahara ne tun a shekarar 2018.

Gwamnatin Spaniya ta ce a wannan shekarar fiye da mutum dubu goma sha daya ne suka isa tsaunukan Canary, idan an kwatanta da mutum 2,557 da aka samu dai-dai wannan lokaci a bara.

Shekarar da aka fi ganin yawaitar ‘yanci rani a baya itace ta 2006, inda aka samu mutum dubu talatin da biyar da suka isa archipelago a cewar Majalisar Dinkin Duniya.

Hukumar kula da al’amuran kaura ta duniya ta ce zuwa yanzu akalla mutum 414 ne aka tabbatar sun mutu a wannan hanya ta zuwa turai.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here