’Yan Najeriya na Cikin Yunwa – Jigon APC ga Tinubu 

 

Wani jigo a jam’iyyar APC mai mulki, Olatunbosun Oyintoloye, ya shawarci Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu kan duba halin yunwar da ya ce ’yan Nijeriya na ciki.

Olatunbosun ya shaida wa manema labarai a Osogbo, babban birnin Jihar Osun ranar Lahadi cewa mutanen Najeriya na cikin yunwa.

Sai dai ya shawarci Shugaba Tinubu da ya yi watsi da rahoton majalisar dinkin duniya cewa za a yi yunwa a kasar nan.

Ɗan siyasar, kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito, ya ce matsin da ake ciki ya hana ’yan kasar da dama ɗora tukunya sau uku a rana.

Daga nan sai ya shawarci Shugaban Kasa Tinubu da ya gaggauta shawo kan matsalar a kasar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here