Tsofaffin Kuɗi: ‘Yan Najeriya na ɗarɗar da Umarnin Kotun ƙoli Kan Ci gaba da amfani da N500 da N1000
A jiya ne kotun ƙolin Najeriya ta yanke hukuncin cewa za a ci gaba da amfani da tsofaffin kuɗin ƙasar har zuwa 31 ga watan Disamban 2023.
Bisa dalilan da ta ce sun ci karo da kundin tsarin mulki da kuma dokar da ta kafa CBN sashe na 20 na dokar 2007.
Kotun ta kuma soke matakin Gwamnatin Tarayya na sake fasalin naira, tana cewa matakin ya ci karo da kundin tsarin mulki na 1999.
Read Also:
A hukuncin da ya yanke a ranar Juma’a mai shari’a Emmanuel Agim, ya ce sahalewar da Shugaba Buhari ya yi wa CBN na janyo takardun tsofaffin kuɗi ba daidai ba ne.
Sai dai wasu al’umar ƙasar da BBC ta tattauna da su, sun ce har yanzu ba su gamsu da wannan umarnin ba, ganin cewa kotun ta sha bayar da umarni a baya kuma ba a bi.
Malam Abba wani mai sayar da kayan marmari a Abuja ya ce “ai sai na ji sanarwa daga CBN ko kuma shugaban ƙasa amma ba yadda za a yi na karɓi waɗan nan kuɗi”.
Wata matashiy cewa ta yi ” ina kuɗin suke bayan sun janye duka tsofaffin kuma babu sabbin a ƙasa ai wannan ba ta sauya zani ba ne,” in ji matashiyar.
Duk da kotun ta bayar da wannan umarni amma yan ƙasar suna cikin zullumi na rashin tabbas.