‘Yan Sanda Sun Gano Yarinyar da Aka Sace a Makota

 

Rundunar ‘yan sandan Kano ta samu nasarar ceto wata yarinya mai suna Amina ‘yar shekaru biyu da rabi.

An ceto ta ne bayan mahaifinta ya shigar da kokensa ga ‘yan sanda cewa wani ya kira shi tare da neman kudin fansar N2m.

Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da ceto yarinyar awanni 16 da sace ta cikin koshin lafiya a makota.

A sanarwar da kakakin rundunar ‘yan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ce an nemi kudin fansa N2m.

An ceto Amina cikin koshin lafiya

Rundunar ‘yan sandan Kano ta bayyana cewa ta ceto Amina awanni 16 bayan sace ta a Sabuwar Gandu, Kwarin Barka da ke Kano.

Jami’an yaki da garkuwa da mutane ta rundunar ne su ka ceto yarinyar bayan binciken kwa-kwaf, jaridar Leadership ta wallafa.

Matashi Zakariyya ya amsa zargin sata Matashi mai shekaru 22, Zakariyya Muhammad ya amsa cewa shi kadai ne ya lallaba ya sace Amina, tare da neman mahaifinta ya biya shi kudin fansa.

Matashin ya bayyana cewa Amina ‘yar makocinsa ce, kuma da kansa ya yiwa jami’in ‘yan sanda jagora har inda ya boye ta a unguwar.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce likitoci a asibitin kwararru na Murtala sun tabbatar da lafiyar Amina kalau.

SP Kiyawa ya nemi jama’a su rika sa ido kan ayyukan bata gari a yankunansu, tare da mika bayanai ga jami’an ‘yan sanda.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here