‘Yan Sanda Sun Kama Wani Mai Wankin Mota
Idris Ayotunde wani matashi ne da ya kammala karatun HND amma bai samu aiki ba.
Hakan ya sa shi yanke shawarar bude wurin wankin mota a kusa da wata tashar mota da ke garin Legas.
Sai dai, matashin ya gaza fin karfin zuciyarsa, ya saurari hudubar shaidan, ya gudu da dankareriyar motar kwastoma.
Wani mai sana’ar wankin mota, Idris Ayotunde, ya shiga hannun jami’an rundunar’yan sanda bayan ya gudu da dankareriyar motar kwastomansa da ya kawo wanki, kamar yadda Punch ta rawaito.
Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ne suka kama Ayotunde bayan ya gudu da motar da aka bashi wanki a jihar Legas.
Ayotunde ya gudu da galleliyar motar zuwa jihar Ogun.
Matashin ya fara sana’ar wankin mota a tashar mota ta Jimoh da ke Shaha, Akowonjo, a jihar Legas bayan ya kammala karatunsa na HND.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Ogun, DSP Abimbola Oyeyemi, ne ya sanar da hakan a cikin jawabin da ya fitar ranar Lahadi.
Read Also:
Oyeyemi ya bayyana cewa mai motar ya kai ta wurin Ayotunde domin a yi mata wankin walkiya, lamarin da ya sa ya bar makullin motar a hannun Ayotunde.
“Ya yi kacibus da jami’an tsaro a kan hanyarsa ta zuwa ya siyar da motar a Ibadan.
“Mai motar, Shofidiya Tosin, ta shigar da korafi a ofishin rundunar ‘yan sanda na Shaha kuma tuni rundunar ‘yan sanda ta tuntube ta tare da sanar da ita cewa an kama Ayotunde,” a cewar Oyeyemi.
annan ya kara da cewa, “jami’an ‘yan sanda ma su tabbatar da tsaro a manyan hanyoyi ne su ka kama mai laifin a kauyen Alakija da ke kan hanyar Abeokuta zuwa Ibadan a yayin da suke gudanar da binciken ababen hawa.
“Sun tsayar da motar tare da tambayar mai laifin ya basu takardu, hakan kuma sai ta gagara, lamarin da ya sa daga bisani aka wuce da shi zuwa ofishin ‘yan sanda Odeda, inda a nan aka gano cewa sato motar ya yi.”
Kakakin ya kara da cewa tuni kwamishinan ‘yan sandan jihar Ogun, Edward Ajogun, ya bayar da umarnin a mayar da tuhumar mai laifin zuwa jihar Legas, inda aka saci motar.