Gwamnatin Kano Tayi Magana Kan Almajiran Jahar

 

Gwamnan jihar Kano, Abdulllahi Umar Ganduje ya bayyana cewa almajiran da ke Najeriya ba ‘yan kasa bane.

Kamar yadda ya sanar, ya ce da yawansu da ke yawo a tituna ‘yan kasashen Nijar, Chadi da Kamaru ne.

Ya tabbatar da cewa kawo tsarin Boko a lamarin almajiranci zai matukar kawo cigaba a fannin ilimi.

Da yawa daga cikin daliban makarantun allo, wadanda aka fi sani da Almajirai, wadanda ke yawo a titunan arewacin kasar nan ba ‘yan Najeriya bane a cewar gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje.

“Da yawansu daga kasashen ketare suke kamar jamhuriyar Nijar, Chadi da Kamaru,” Ganduje yace yayin bude taron kwanaki uku da UBEC take a jihar Kano.

“Daga binciken da muka yi, da yawa daga cikin almajiran da ke yawo a titunanmu daga kasashen Nijar, Cahdi da Kamaru suke.

“Matukar aka inganta yanayin karatun Almajiri, za a janyo almajiran ne daga sauran jihohin. Wannan kuwa ba matsala bane.

“Gwamonin arewa suna matsawa wurin samar da dokar da za ta hana lmlajirai shiga wata jiha daga ta su,” yace.

Ganduje ya bayyana cewa, karatun firamare da na sakandare zai zama kyauta kuma dole, hakan ne kadai hanyar gyara tsarin almajiranci inda za a bai wa bangaren ilimi fifiko, Daily Nigerian ta wallafa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here